"Deeya! Kinsan kin mini laifi ko?"
Ta narkar da murya,lokacin da Jamila ta fito suka sakarwa murmushi.
"Nasan ban kyauta ba yaya j,ayimin afuwa."
Ya sauke ajiyar zuciya har tana jiyo hucinsa,
"I miss you so much wallahi,Deeya inajinki a raina fiye da tunaninki. Please yaushe zakimin iznin zuwa gidanku?"
Yayi furucin ba tare daya shirya ba,zai iya rantsuwa ba tare da kaffara ba,yayi kewarta sosai. Burinsa bai wuce ya ganta ba ya kuma san kowacece.
Ladi tayi shiru gabanta yana fad'uwa.
"Deeya"
Ta dubi Jamila wacce ke sallah,
"Na'am."
"Meyasa bakyason mu had'u ne? Kina zaton zumuncinmu zai cigaba da kasancewa a haka ba tare da mun had'u da juna ba?"
Ta lumshe ido,ai tafishi son yasan da zamanta. Tafishi son zumuncinsu yafi haka nisa.
"Kinyi shiru."
Ta numfasa "Kayi hakuri yaya j,lokaci ne. Da kaina zan maka izni zuwa gidanmu."
"Har yaushe ne Deeya? Sai kinga na fad'i ba rai ko?"
Baisan lokacin da yayi furucin ba,saidai yasan hakika yana jin Hadiyya a ransa sosai. Baya zaton sonta yakeyi,duk da dai yanayin da yakeji a ransa game da ita makamancin yanda yakejin SIYAMA ne.
Ta dauke wuta d'if na 'yan dakiku,maganarsa take nanatawa a zuciyarta cike da mamaki. Gani takeyi kamar a mafarki,me yake nufi?
"Yanajin abunda nakeji?"
Har batasan sadda maganar dake zuciyarta ta fito fili ba.
"Kema kina jina a ranki dagaske Deeya?"
Ai batasan lokacin data mike tsaye ba har Jamila wacce ke addu'o'i ta dubeta a razane.
"Lafiya?"
Ta rufe baki saboda dariyar farin ciki daya taho mata. Ta girgiza mata kai tare da shige band'aki.
"Ina jinka sosai yaya j,fiye da tunaninka."
Yayi shiru kad'an kafin yace
"Nagode deeya,nagode. Saikiyi kokari ki bani iznin zuwa gidanku don Allah. Kinji ko?"
"In sha Allah yaya j,ka d'an bani lokaci kaima."
"Shikenan Deeya,bari na barki haka."
"Toh yaya j,agaishemin da antina da bebina."
"Zasuji in sha Allah."
Daga haka sukayi sallama,tayi hamdala yafi sau biyar sannan ta fito. Jamilah ta ajiye darduma akan katifarta.
"Wai yau wane mai sa'an ne da har ya samu kika saurareshi?"
Ta harareta tana dariya
"Oho maki,nidai saida safe. Nasan mama tana can tana fushin dad'ewata."
Jamila tayi dariya
"Au dama ba hira kikazo muyi ba? Lallai ma,muje na rakaki toh tunda na gane waya ta tsayar dake."
Ladi ta lumshe ido kad'an kafin ta bud'esu tayi gaba. Hajiya hindatu bata falon don haka tayi gaba,har saida suka d'anyi nisa da tafiya ita da Jamila kafin tayi mata sallama ta k'arasa.
Mama tayi fad'an dad'ewarta,kafin kuma ta sauko ta hakura.
Ranar bacci b'acci b'arawo ne kawai ya sace Ladi,abunda ke gabanta bai wuce kiran Basma ba domin neman shawarar yanda zata warware kanta awajen Jafar.
*********
Tun daga wannan ranar,waya bata yankewa tsakanin Jafar da Hadiyya....
har ya zamana zuciyoyinsu sun gaza b'oyewa junansu sirrikan dake mak'ale a cikinta. Ga Jafar,jinshi yake tamkar a wata sabuwar duniya. Tun sadda akalar hirarsu ta raja'a akan(no Hausa..)akan SOYAYYA sai yake ganin Deeyarsa kamar wata sabuwar halitta. Muryarta ta k'ara zak'i a dodon kunnuwansa haka ma zantukan da suke musayarsu ta sak'onni ya zamana daban. Har yakan yi mamakin yanda akayi ta iya kalaman soyayya masu dad'i haka.
Ga Ladi kuwa,tsoro da fargabar ranar da k'arya zata k'are bai fiye bata damar jin k'arfin gwuiwa akan soyayyarsu ba. Takanji zuciyarta ta karye, hawaye sukan yawaita zubo mata duk ranar da suka kammala wayarsu da Jafar sukayi sallama. Ta ina zata fara ne? Gashi a gefe guda ta bar samun Basma a waya ta yanke shawarar zuwa gidansu don jin dalilin rashin samun layin wayarta daga bakin innarta.
Hakan kuwa tayi,tasowarta daga makaranta ta nufi unguwarsu Yakasai. Kafin ta soma zuwa gidansu kawai sai ta nufi gidansu Basma. Taci sa'ar samun innarta a gida. Bayan gaisuwa ta nemi sanin dalilin rashin samun Basma. Inna tace
"Oh ni Dije,ina zan kai mantuwa ne? Kinga kuwa ko d'azun nan munyi magana tace na baki lambarta na yanzu wai bata samunki. Shima Haruna(kanin Basma)ya sanya wasa ne shiyasa bai tunasar dani na rubuta na bashi ba. Ga wayar akan kujera,shiga ki d'auko."
Da azama Ladi ta fad'a falon inna. Ta dauko wayar,tana karb'ar wayar tayi niyyar tafiya. Ba yanda ta iya dole ta tsaya ta karb'i tayin abinci da ruwan da inna tayi gareta.
*****
Ringing d'aya biyu,Basma ta dauka.
"Shegiya tawan, nayi kiranki yafi sau goma amma na rasa dalilin da network bai aminta da zumuncinmu ba. Ya gari?"
Ladi tayi dariya
"Gari kalau,nima kwana biyu bana samunki dole saida na biya wajen inna d'azu domin naji ko lafiya. Ya karatu?"
"Gashinan muna fama,kedai bari kawai. Ina mama da mutuminki?"
Ladi ta muskuta akan kujerar da take zaune tana nazarin aikin makaranta
"Mama lafiya. Ai a kanshi ne nake ta cigiyarki."
"Toh fa,ba dai kwab'armu ce tayi ruwa ba?"
"Ta kusa dai matukar bamu kula ba Basma."
Nan ta labarta mata halin da suke ciki
"Nifa ina tsoron yi mishi iznin zuwa wajena Basma. Kunya kam a ajiye batunta gefe,don tun fara gudanar da wannan tsarin nasan da zamanta komai daren dad'ewa. Fargabana bai wuce Yaya J ba,anya bazai gujeni ba?"
Basma tace
"Haba ya kike wannan tunanin? Inace kin gama tabbatar da cewar yana maki son da bazai iya fiddaki a ranshi ba?"
Ta gyada kai
"Na fahimci hakan kamar yanda shima ya sha fad'amin."
"Alhamdulillah,shawarar da zan baki kawai ki bashi damar zuwa wajenki. Matukar kika dunga zillewa bana maki fata, saidai nasan da wuya idan nazai fice daga sha'aninki ba. Kawai yazo,idan ma hakuri ne ki bashi. Zan tayaki da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai."
Ladi ta amince da maganganun Basma,bugun zuciyarta ta d'an ragu. Basma bata tab'a bata shawarar data bi tazo tayi dana sani ba don haka ta amince.
"Shikenan aminiya, zanyi amfani da zancenki."
"Haba ko kefa? Kada ki damu komai bazai gagari Ubangiji ba. Mu dage da addu'a tunda da zuciya d'aya muka aikata niyyarmu. Ina ita Siyamar take da kike cewa har da dare kuna waya?"
"Ta haihu,gobe ne suna. Har ya sanar dani sunan yaron ma."
Sukayi dariya,Basma tace
"Kinji fa? Ashe kaunar har ya wuce tsammanina. Allah Ya kaimu toh."
"Ameen."
Suka shiga hirarsu ha kud'in Ladi ya k'are, Basma ta biyo baya tamkar kada su rabu.
******
RANAR SUNA.....!
Yaro yaci suna Umarul Faruk. Ranar anyi buduri sosai. Su Anti Habiba ma da matan DM ba'a barsu a baya ba.(lol). Ranar kam Siyama ta fito sak da ita babu wanda zai kalleta yayi kiranta da sunan Kazama.
Jafar ma yinin gidansu yayi don ranar baiyi nisa ba. Yana nan tare da Haris wanda shima ya kawo Ummi da Rahma amaryarsa wajen sunan. Har Jafar yana tsokanarsa
"Kaga angon Rahma uban 'ya'yan Ummi. Wato dai Allah Ya taimakeka kan matanka ya had'u hankali kwance sai mulmula uban k'iba kakeyi."
Sukayi dariya,Haris yace
"Ba dole ba. Ai Ummina ta shayar dani mamaki. Ban tab'a zaton haka zata dauki lamarin da sauki ba. Kasan farko farkon nan daman sai namiji yayi hakuri saboda dole ne daman su nuna kishinsu. Ita kanta Rahma da make tsoron kada ta rikitamin gidana sai gashi ta bani mamaki ba k'ad'an ba. Tana bin Ummi tana bata girmanta a matsayinta na yayarta."
Jafar yayi murmushi
"Dole hankalinka ya kwanta."
Cikin tsokana yace
"A'a toh,kaidai zauna kada kayi auren nan."
Jafar ya shafi sumarshi yana murmushi
"Bar batun auren nan a gefe."
Haris yana kallonshi yace
"Ina kanwarka ta waya?"
Jafar ya gyara zamanshi akan motar Haris
"Ka tab'omin inda yakemin k'aik'aiyi. Ita nake zurawa ido. So nakeyi tayimin iznin zuwa gidansu mu gaisa kaga sai zumunci ya d'ore."
Haris yayi dariya yayi dariya,Jafar ya daure fuska
"Zaka fara ko? Menene na dariyar?"
Haris ya girgiza kansa
"Akwai wata a k'asa tsakaninka da kanwarnan taka. Duk yanda akayi dai sonta kakeyi."
Jafar ya kauda kansa gefe,ba tare da ya dubeshi ba ya tab'e baki yana d'aga kafad'a
"Zai iya yiwuwa hakan ne. Kasan har yanzu bana gane feelings na So. "
Haris ya d'an bugi kafad'arsa yana dariya,har saida ya bawa Jafar dariya. Yana murmushi ya kalleshi
"Mene abun dariya? Kaifa d'an iska ne. Toh idan ma sonta nakeyi akwai wani abu a ciki?"
Sukayi dariya,Haris ya nunashi da yatsa
"Gwara dai daka fad'i gaskiya. Amma babu wanda zai tsaya har yayi mintuna yana sauraron hirarku yace wai ba soyayya kukeyi ba. Kaidai kace mun kusa shan biki."
Har lokacin murmushi bai yanke daga fuskar Jafaru ba. Ya sauko daga saman motar
"Ya danganta."
Haris dariya yakeyi,ya gama yarda amininsa ya fad'a tarkon soyayya sai fatan Allah Ya sanya alheri. Ashe dai shiyasa ba'ason mutum ya zama mai CIKA BAKI,gashi dalilin hakan Allah Ya jarabceshi da son wata bayan Siyamar da yake ikrarin bazai tab'a son wata bayanta ba.
*******
Ranar Alhamis,itace ranar da Ladi ta yiwa Jafar iznin zuwa gidansu. Farin ciki da d'okin son ganinta sun hanashi sakat. Wannan yasa a daren litinin bayan magriba yana isowa gidansa. Yayi wanka abinsa ya shirya cikin manyan kaya banda babbar riga. Ya feshe jikinshi da turare sannan ya fito ya soma haramar tafiya.
Tunda yayi kiranta a waya ya sanar mata isowarsa ta tsinci cikinta da rud'ewa,gaba d'aya ta kasa nutsuwa har saida ta ziyarci band'aki ta rage cikinta. Ta fito ta k'ara duban fuskarta madubiduk da kwalliyar data sha wannan baisa tabar fidda gumi ba. Kai k'arya batayi ba rayuwa. Mama tana daga zaune tana kallonta cikin nazari
"Wai yau wane mai sa'an ne har ake ta gyare gyaren fuska saboda shi?"
Ladi tayi dariyar yak'e
"Lah,Mama wanda kike yawan jinmu muna waya ne fa."
Mama tayi murmushi
"Ikon Allah,shine zaizo kenan? Allah Ya kawoshi lafiya. Saiki kama kanki duk da dai bansanki da rawar kai ba."
Hamidah tayi murmushi
"Toh Mama zan kiyaye."
Kafin Mama tayi magana wayar Ladi tayi k'ara,ta amsa cikin jin fargaba. Jafar ke sanar da ita ya iso kantin datayi mishi kwatance dashi.
"Toh zaka ga wani gida daga gefen hagun kantin,nan ne gidan. Ganinan fitowa yaya j."
Sukayi sallama,ta juya ta dubi mamanta,sukayi murmushi. Na Ladi kam baije ko'ina ba domin ita kad'ai tasan yanda hantar cikinta ke kad'awa.
"Mama saina dawo."
"Toh kada ki zauna,ku tsaya nan jikin gidan."
"Toh."
****
Hankalinsa yana kan k'ofar,zuci zucin ganin Deeya yake. Burinsayayi tozali da ita.
A sannu ya dunga jin k'amshi yana bugar hancinsa,wannanya k'ara sanya Jafar tattara hankalinsa ga k'ofar,murmushinsa mai bayyana hakoransa yake fitarwa. Ji yakeyi kamar ya fad'a zauren ya janyota waje. A sannu ya hangi kafarta na dama ya soma fitowa kafin ita d'inma ta fito gaba d'ayanta. Baisan lokacin daya mik'e daga kan mashin d'insa ba...
Koya abin ze kasance..!???