Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya bayyana kasar a matsayin kasar Musulunci, kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a kasar, inda ya kara da cewa yanzu ba su da wata alaka da dokokin zamanin mulkin mallaka.
Shugaba Jammeh ya bayyana hakan ne a gidan talabijin din kasar.
Ya ce babu wasu dabi'un da suka sabawa Musulunci da za a bari ana gudanar da su a kasar ba tare da an dauki mataki ba.
Kusan kashi casa'in cikin dari na 'yan kasar Musulmai ne. Sannan kuma Jammeh ya soma shugabancin kasar ne shekaru 21 da suka gabata.
"Kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a kasar, Gambia ba za ta sake kasancewa cikin dokar mulkin mallaka ba", inji shugaba Jammeh.
Idan a za a iya tunawa a shekarar 2013, Jammeh ya janye kasar Gambia daga cikin kungiyar kasashe renon Ingila, inda ya bayyana kungiyar a matsayin ta mallaka.
Title :
Kasar Gambia Ta Dawo Kasar Musulunci
Description : Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya bayyana kasar a matsayin kasar Musulunci, kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a kasar, inda ya kar...
Rating :
5