"Idan ka yi duba da irin laifukan da mutanen nan suka aikata a kasar nan, babu yadda za a yi a bada belinsu"
"Dasuki ya yi ta watanda da dukiyar gwamnati yadda ya ga dama. Kawai za su cewa babban bankin kasa ne suna bukatar bilyan 40 ko fiye da haka ba tare da wata hujja ba a diba a ba su".
"Don haka kuskure ne a ce an bada belin Dasuki domin ya je Landan duba lafiyarsa. Yayin da muke da sama da mutane milyan biyu jibge a sansanin 'yan gudun hijira, wadanda akasarinsu sun zama marayu. Idan muka yi haka wace irin gwamnati ke nan muke tafiyarwa? Ba za mu taba amincewa da haka ba".
Buhari ya bayyana hakan ne a hirarsa da 'yan jaridu a jiya.
Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, wanda shine tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathqn shawara kan harkar tsaro, ana zarginsa ne da karkatar da sama da dala bilyun biyu da doriya da aka ware domin sayen makaman yakar Boko Haram
Title :
Kalaman Buhari Akan Sambo Dasuki
Description : "Idan ka yi duba da irin laifukan da mutanen nan suka aikata a kasar nan, babu yadda za a yi a bada belinsu" "Dasuki ya yi t...
Rating :
5