Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana a yau Litinin cewa matsalar layin man fetur da ake fama da shi a yanzu a duk fadin kasar nan, gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ce sila.
Lai ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala taron mukarraban gwamnati, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati a Abuja.
Ministan ya ce tun a cikin watan Agusta, 2014 ya kamata Jonathan ya daidaita batun janye tallafin mai.
Title :
Jonathan Ne Silar Wahalar Man Fetur Da Ake Ciki A Yanzu, Inji Lai Mohammed
Description : Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana a yau Litinin cewa matsalar layin man fetur da ake fama da shi a yanzu a duk fadin kasar nan...
Rating :
5