Shugaban rundunar sojojin Nijeriya na kasa, Janar Tukur Buratai ya tsallake yunkurin halaka shi a yau Asabar, a yayin da mabiya Shi'a suka yi arangama da rundunar sojoji.
Rundunar sojojin ta kasa ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter.
Bincike ya nuna cewa kimanin mutane bakwai ne daga cikin membobin Shi'an suka rasa ransu a yayin artabun.
Har dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, majiyarmu ta Vanguard ba ta tabbatar da musabbabin aukuwar lamarin ba.
Title :
Janar Buratai Ya Tsallake Yunkurin Halaka Shi A Yayin Artabun Sojoji Da 'Yan Shi'a A Kaduna
Description : Shugaban rundunar sojojin Nijeriya na kasa, Janar Tukur Buratai ya tsallake yunkurin halaka shi a yau Asabar, a yayin da mabiya Shi'a s...
Rating :
5