DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Jam'iyyar APC ta jihar kaduna, ta dakatar da Sanata mai wakiltar mazabar dan majalisar dattawa na kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani daga jam'iyyar gaba daya.
Sanarwar dakatarwar na kunshene a cikin wata takarda wacce ta samu sanya hannu Aminu Abdullahi a matsayin shugana jam'iyyar na matakin unguwar Tudun wada ta arewa, wato mazabar Shehu Sani, sai kuma sa hannun Auwal Mai unguwa a matsayin Sakatare, da Aminu Alilan wanda yake matsayin jami'in hulda da jama'a.
Sanarwar ta bayyana cewar, an yanke shawarar dakatar Shehu Sani daga jama'iyyar ne, biyo bayan wani zama da akayi a ranar 27 ga watan Disambar nan da muke ciki, inda aka zayyano manya manyan zunubbai da Shehu Sani ya aikatawa jam'iyya da gwamnatin jihar kaduna karkashin Nasiru El Rufa'i.
Sanarwar ta bayyana cewar Sanatan ya zamo tsagera wanda yake yawan kai farmakin ga gwamna El Rufa'i, da kuma karan tsaye gami da dagawa da yakeyiwa shugabancin jam'iyyar a jihar.
Sannan sanarwar ta soki lamirin wadanda ta kira 'yan koren Shehu Sani, wadanda basu komai sai kiran taron manema labarai a kusan kowane mako suna la'antar shugabancin jam'iyya da salon mulkin gwamna El Rufa'i.
Sannan sanarwar ta kara suka mai tsanani ga Shehu Sani, inda tace baya gudanar da aikin da jama'ar mazabarshi ta turashi na wakilci a majalisa, ya maryar da hankali kawai wajen sukan gwamnatin El Rufa'i, da shugabannin jam'iyya a jihar.
Dakatarwar za ta dauki tsawon watanni goma sha dayane, kafin aga matakin da za'a dauka anan gaba,
Title :
Jam'iyyar APC Ta Jihar Kaduna Ta Dakatar Da Sanata Shehu Sani Daga Jam'iyyar
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Jam'iyyar APC ta jihar kaduna, ta dakatar da Sanata mai wakiltar mazabar dan majalisar dattawa na kaduna t...
Rating :
5