Tambaya ???
Assalamu alaikum Malam mutum ne matarsa ta dauki abinsa, sai yace kodai ta dawo da abin data dauka ko kuma ya saketa, ita kuma zafin wannan maganar da yayi, sai tace bazata dawo da abin ba, sai yace ya saketa, sai tace masa saki nawa, sai yace konawa takeso, sai tayi shiru ba tace komai ba, sai yayi maza ya shedama mahaifinta abinda yafaru, da cewa yasata, ta maido da abin data dauka domin ya warware kalamin da yayi, daga qarshe ta maido da abin.
Malam matsalar anan shine matar tace ya saketa amma shi yace bai sake tava Allah ya san zuciyar shi, idan harta dawo mashi da wannan abun ,toya warware kalamin sakin da yayi.
Matar ta tsayu akan sakine amma shi yace ba sakine bane.
Mallam don Allah menene gaskiyar wannan lamari ?
Allah yasaka da alkhairi.
(Daga Salisu Mahmoud).
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Abin da yake daidai shine sakine, saboda niyya bata da tasiri a saki, ana amfani ne da furuci ma'ana (Abin da miji ya furta).
Sannan ya rataya sakin da wani abu, kuma abin ya tabbata, daga baya kuma yazo ya furta, don haka ta saku.
Allah shine mafi sani.