Daga Saifullahi M. Kabir
↓
Bayan kashe 'yan kasa sama da mutum 2000 da jami'an sojin Nigeria suka yi a Zaria a ranekun Asabar da Lahadi bisa zargin tare musu hanya da aka yi, da rushe ginin Husainiyyah Baqiyatullah, Makabartan Darur Rahma da kuma gidan Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria, Malam Ibraheem Zakzaky. Yanzu haka kuma Jami'an tsaron Sojin na cigaba da tare mutane a hanyoyi suna bincikensu, da zaran sun ga a wayar mutum akwai wani alami na addini musamman na Shi'anci sai su kashe shi.
↓
"Da zaran sun ga wayarka da hoton Alzakzaky , Komaini ko wani a cikin Malaman Yan Shi'a sai su harbe mutum. Haka kuma da sun ga zobe a hannunka sai suce kai ma Shi'a ne. Haka kuma da sun ga mutum biyu ko uku a cikin motar da bakaken kaya sai su bindige dukkan mutanen cikin motar." A cewar wani ganau.
↓
"A gabana Sojoji suka kashe wasu mutane moto guda saboda sun ga mutum biyu da bakaken kaya da wata mace da bakin hijabi karami" Inji wani da ya fito daga Kano zuwa Kaduna.
↓
Tuni dai rundunar na Sojojin Nigeria suka bayyana cewa an kai musu hari ne inda Shugaban nasu ya tsallake rijiya da baya. Amma kuma daga baya da kan su suka musanta wannan zargin na farko da suka yi, yayin da suka dawo suka ce an tare musu hanyar wucewa ne a yayin da ake taro a muhallin taron na Yan Shi'a.
↓
Tambayar da masu hankali suke yi Shine; Idan an tare hanya saboda ana taro sai a bude ma al'umma wuta a kashe sama da mutum dubu uku, a rusa gine gine?
↓
Anji rundunar ta Soji suna cewa sun kai karar tare hanyar da aka musu ga kungiyar kare hakkin bil adama. "Me yasa tun farko ba su dauki wannan matakin ba da aka tare hanyar suka ga ba a wucewa? Sai da suka yi barnar da ba gaira ba Dalili sannan za su kai kara?" -Inji wani dake bayyana ra'ayinsa.
↓
"Wane irin Jifa ne Jonathan bai sha a garin Bauchi ba? Yana matsayin Shugaban kasa ma. Amma sai ya kashe mutanen Bauchi? Ko mutum 1 bai sa an bude wuta ba. Dan me tsare ma 'Dan kasa guda 1 da zai jawo kashe sama da mutum 3000 da kuma rusa gine gine?" Inji wani dan garin Bauchi.
↓
Wani kuwa ya shaida ma al'umma a shafinsa na facebook cewa; "Wace kungiya ce bata tsare hanya a kasar nan idan suna gabatar da ibadarsu? Awa nawa ne duk ran Lahadi Chritocin kasar nan sukan rufe hanyoyi da ko Shugaban kasa ne yazo wucewa sai dai ya bi ta wani wajen? Duk ranar Juma'a hanyoyin da suka bi masallatan Juma'a kulle su ake yi. Hatta idan za ka yi tafiya akan babban hanyoyi a wasu garuruwan kullesu ake yi sai mutum ya jira an gama sallar Juma'a. Sau nawa Yan Siyasa da masarautu ke tarukansu a gari ya zama garin sam ba hanyoyin wucewa, sai aka taba budewa waye Wuta? Wane Sarki aka taba Yunkurin kashewa da rusa masa gini ko Liman ko Pasto dan kawai mabiyansa sun kulle hanya saboda harkokin Tsaron lafiyar mahalarta taronsu?"
↓
Wani abu da ke kulle ma al'amma kai shine, Me ya hada Sojoji da alamomin addini irin Zobe da bakin riga ko Hijabi, hoto ko Wa'azi a waya yasa suke kashe mutane? Dama suna fada da Shi'anci ne?"
↓
Wani ganau ya shaida min cewa ya ji da Kunnensa yadda Sojojin da suke rusa gidan Malam Zakzaky suna saka masa wuta suna kara harbin wadanda ba su karisa Rasuwa ba bayan sun harbe su a unguwar, a daidai sadda suke wannan aikin sun cigaba da cewa " Ba Shi'a ba kayanta! Mun yi maganin Shi'a yau. Sai dai wasu ba su ba...."
↓
Kenan ashe duk Malaman da suke fatawar a kashe Shi'a a masallatansu har ma suke ba yaransu adda suna kai hare hare akan Yan Shi'a da Tada Bom kenan Sojojin Nigeria ne suke saka su?
Zaku Iya Tura mana na Ku Labarai ta shafin Mu na FACEBOOK
Title :
HAR YANZU JAMI'AN TSARON SOJOJIN NIGERIA NA CIGABA DA KASHE MUTANE A ZARIA
Description : Daga Saifullahi M. Kabir ↓ Bayan kashe 'yan kasa sama da mutum 2000 da jami'an sojin Nigeria suka yi a Zaria a ranekun Asabar da L...
Rating :
5