lokacin sanyi ne yakamata mata su zama kullum suna makale ajikin oga to amma idan jikinki ya zama babu wani laushi babu dumi sai kiga ana juya miki baya ya kamata kiyi yanda mijinki kullum yana kankame dake shine naga dacewar maimaita bayanin domin zai iya zama sabo a wajen wadansu
Ki samu ayaba mai kyau ki bare ko ki matse da hannunki ko ki markada yayi laushi sai ki zuba madara peak ki fasa kwai amma farin zaki zuba banda jan ki matsa lemon tsami ki gauraya sosai sai ki shafa a jikinki yayi sa a daya (1hour) sai kiyi wanka da ruwan zafi amma ba zafi sosaiba Idan kinayin wannan har kwana uku zakiga yanda jikinki zaiyi
sannan zaki iya daka ganyen magarya ki zuba cikin man zaitun ki hada da man habbatussauda sai ki dinda shafawa ajikinki bayan sa a daya (1hour) sai kiyi wanka fatarki zatayi laushi
haka kuma sabulun salo shima ana hadashi da ganyen magarya a kwabashi da man habbatussauda dan kadan bayan ya hade ya zama sabulu saiki rinka wanka dashi shima yana gyara fata sosai jikinki yayi laushi.
Title :
Gyaran Jiki Mata
Description : lokacin sanyi ne yakamata mata su zama kullum suna makale ajikin oga to amma idan jikinki ya zama babu wani laushi babu dumi sai kiga ana ju...
Rating :
5