Gwamnatin tarraya a jiya Talata ta tuhumi tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki, tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarwa da dansa Sagir da laifuka 43.
Sauran wadanda hukumar EFCC ta ke tuhumar su a madadin gwamnatin tarayya, sun hada da shugaban kamfanin gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi, tsohon daraktan kudi a ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Shu'aibu Salisu da Aminu Baba Kusa.
Kowanne daga cikin su ana zargin ya wawushi bilyoyin kudaden da aka ware domin sayen makaman yakar ta'addanci ne a lokacin gwamnatin da ta shude.
An shigar da karar ne a kotun daukaka kara, amma har yanzu ba a yanke wani hukunci ba, kamar yadda majiyarmu ta rawaito.
Source Rariya
Title :
Gwamnatin Tarayya Na Tuhumar Dasuki, Barafawa Da Dokpesi Da Laifika 43
Description : Gwamnatin tarraya a jiya Talata ta tuhumi tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki, tsohon karamin minist...
Rating :
5