DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
An bayyana rade radin da jama'a ke yadawa na cewar wai gwamna El Rufa'i zai kaddamar da rusau, a cibiyar 'yan kilishi dake unguwar Sarki a garin Kaduna, da cewar labarine na kanzon kurege wanda bayada tushe ballantana makama.
Shugaban masu sayarda kilishi na unguwar sarki, Alhaji Sa'idu Mai Kilishi ya tabbatar da haka, a yayin da yake zantawa da RARIYA a cibiyar 'yan kilishi dake kaduna.
Sa'idu mai Kilishi ya kara da cewar, gwamna El Rufa'i masoyinsu ne tunda dadewa, tun zamanin yana Minista a birnin tarayya Abuja, inda ya shigo kaduna to yana yada zango a cibiyar 'yan kilishin ya sayi kilishi mai yawan gaske, kuma har a yanzu da yake matsayin gwamna haka abin yake.
Sa'idu mai kilishi ya kara da cewar, abinda ya tabbata akan wurin sana'arsu ta sayar da kilishi, wacce tun zamanin Sardauna iyayensu ke sana'a a wannan waje, har ya zuwa lokacin da suka gajesu, gwamna El Rufa'i ya tabbatar musu da cewar za'a inganta musu wajen sana'ar tasu ya dace da yanayi na zamani.
A kwanakin baya ne jama'a keta yayata batun cewar wai gwamna Nasiru El Rufa'i, na wani shiri na ruguza cibiyar 'yan kilishin dake unguwar Sarki, domin fadada hanyoyi.
Title :
Gwamna ElRufai Ba Zai Tada Masu Sayar Da Kilishi Dake Unguwar Sarki Ba, Inji Shugaban Masu Kilishi A Yankin
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA An bayyana rade radin da jama'a ke yadawa na cewar wai gwamna El Rufa'i zai kaddamar da rusau, a cibiy...
Rating :
5