A kokarin da rundunar sojojin Nijeriya ke yi don ganin sun kakkabe dukkanin sansanin 'yan Boko Haram, Burgediya na 25 na dakarun sojojin Nijeriya sun yi nasarar kakkabe wata mafakar 'yan ta'addan dake daidai titin Damboa-Njaba-Bale a jihar Borno.
Sojojin sun yi nasarar kashe 'yan boko haram guda uku wadanda suka addabi mazauna yankin Sabon Gari da Damboa. Amir din 'yan ta'addan na daga cikin wadanda aka kashe a kauyen Bulayaga.
Amir din ya shahara wajen tada hankulan mazauna yankunan Bale, Wass da Mufurundi.
Sojojin sun kuma kwace makamai da dama daga wurin 'yan bindigan.
A wani labari makamancin haka ma, dakarun shiyya ta 7 sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda tara a wani kauye da ake kira Mainari a karamar hukumar Mafa.
Kanal Sani Usman Kukasheka, wanda shine dakaraktan yada labarai na rundunar shi ya bayyana hakan.
Title :
Graphic Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe Amir Din 'Yan Boko Haram Da Wasu
Description : A kokarin da rundunar sojojin Nijeriya ke yi don ganin sun kakkabe dukkanin sansanin 'yan Boko Haram, Burgediya na 25 na dakarun sojojin...
Rating :
5