Rahotanni daga Najeriya sun ce an kashe biyar daga cikin mutanen da ke goyon bayan Nnamdi Kanu, mutumin da ke son kafa kasar Biafra a birnin Onitsha.
'Yan sanda sun tabbatar da harbin mutane da ke zanga-zanga, sai dai sun ce uku daga cikinsu ne suka mutu.
Sun zargi masu zanga-zangar da ji wa wani soja rauni da kuma lalata bindigarsa.
Lamarin ya auku ne bayan wata kotu da ke Abuja ta bayar da umarni a saki Mista Kanu ranar Alhamis, lamarin da ya sa masu goyon bayansa suka rika murna.
Ana zargin Mista Kanu da watsa labaran da ke harzuka mutane a gidan rediyonsa na Biafra.
Title :
Graphic Photos: Mutane Biyar Sun Rasa Rayukansu Yayin Murna Sake Nnamdi Kanu
Description : Rahotanni daga Najeriya sun ce an kashe biyar daga cikin mutanen da ke goyon bayan Nnamdi Kanu, mutumin da ke son kafa kasar Biafra a birnin...
Rating :
5