Gobe Laraba (30/12/2015) idan Allah ya kai mu ake sa ran Shugaban Kasa Buhari zai yi tattauna kai tsaye da wasu zababbun 'yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi kasat nan.
Gidan talabijin (NTA) da gidan rediyo (FRCN) na tarayya za su yada tattaunawar kai tsaye wanda za a soma da misalin karfe tara na dare kamar dai yadda sanarwa da ta fito daga hannun mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ta nuna.
Title :
Gobe Za A Yi Tattaunawar Kai Tsaye Da Shugaba Buhari
Description : Gobe Laraba (30/12/2015) idan Allah ya kai mu ake sa ran Shugaban Kasa Buhari zai yi tattauna kai tsaye da wasu zababbun 'yan jaridu da...
Rating :
5