Assalamu Alaikum, malam fatar kuna lafiya. Malam don Allah ku taimaka min wata na tara da aure har yanzu ban samu ciki ba.. kuma rashin cikin.yana min barazana ga aurena. Iyayen mijina sun sani a gaba wai bana haihuwa. Don Allah ku taimaka min.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuhu.
Lallai hakika wannan Jarrabawa ce daga Allah. Amma kun nuna rashi ln hakuri daga ke har surukan naki.
Shin Qa'idah ne cewar dole sai Mace ta samu Juna biyu tun ashekarar da akayi aurenta??
* Shin sun manta cewa Allah ne yake bada haihuwa, Ba wai kokarin mutum ba??
* Shin basu tunanin cewar zata yiwu 'Dan nasu (Wato Mijinki) shine yake da matsala??
* Shin Matsayinsu na musulmai ba zasuyi koyi da manyan Annabawan Allah irin su Annabi Ibraheem, Annabi Is'haaq, Annabi Zakariyya (alaihimus Salam) wadanda sun haura Shekaru Hamsin da aure kafin Allah ya basu haihuwa!!
Kar ki damu. Ke dai ki sanya tsoron Allah acikin lamarinki kuma kibi mijinki sau da Qafa. Sannan ki dage sosai wajen kulawa da ibadah.
Ga wasu addu'o'i nan ki rika yinsu acikin Sujadarki :
رب هب لي من لدنك ذرية طيبة إنك سميع الدعاء.
رب لا تذرنى فردا وأنت خير الوارثين.
robbi Hablee min Ladunka Dhurriyyatan Tayyibah. Innaka Samee'ud Du'a'i.
Robbi la tadharnee Fardan wa 'anta khayrul Waritheena.
Wadannan sune irin addu'o'in da Annabin Allah Zakariyya (as) ya rika yinsu alokacin da yake naman haihuwa. Kuma Allah ya amsa masa ya bashi Yaro Namiji mai albarka wanda ya zamanto Annabi ne kuma Mursali. (Wato Yahya a.s).
Idan kuma kina da dama ki nemi Man Albabunaj ki rika yin matsi dashi. Sannan kina dafa Furen Albabunaj din kina yin Shayi (tea) dashi.
In sha Allahu mahaifarki zata bude, Kuma Kwayayen halittarki zasu daidaita. Koda akwai sharrin Shaitanun Aljanu to Allah zai taimakeki akansu.
Domin shi Albabunaj yana wanke Marar mutum, yana kashe kwayoyin chutar da suke hana mutu. haihuwa, Sannan kuma yana Qona shaitanun Aljanu masu hana haihuwa.
Sai dai wannan Koren abun da wasu shaguna suke sayarwa fa, ba shi ne Albabunaj ba. Shi ainahin Albabunaj Yellow ne kalarsa.
Allah yasa mu dace. Aameen.
WALLAHU A'ALAM.
Source ZAUREN FIQHU
Title :
Ga Addu'a Dan Samun Haihuwa
Description : Assalamu Alaikum, malam fatar kuna lafiya. Malam don Allah ku taimaka min wata na tara da aure har yanzu ban samu ciki ba.. kuma rashin ciki...
Rating :
5