Kwamitin tabbatar da’a da binciken rashawa da ta dabaibaiye hukumar FIFA ya dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini daga shiga sha’anin kwallon kafa na tsawon shekaru 8, yana mai cewa sun ci mutuncin matsayinsu kan badakalar wasu kudade da Blatter ya biya Platini.
Sannan an ci Blatter tarar kudi dala dubu hamsin wanda ya shafe shekaru yana jagorantar FIFA tun a 1998, yayn da kuma aka ci Platini tarar kudi dala dubu tamanin.
Ana zargin Blatter da amincewa da wasu kudade dala miliyan biyu zuwa ga Platini 2011.
Wannan ya kawo karshen rayuwar Blatter a duniyar kwallon kafa da ya shafe shekaru 17 yana jagoranta.
Hukuncin na yau ya haramtawa Platini neman kujerar shugabanciin FIFA a zaben hukumar da za a gudanar a ranar 26 ga watan Fabrariu.
Jami’an FIFA masu gudanar da binciken sun nemi a haramtawa Blatter da Platini shiga harakar kwallo na har a abada, ko da ya ke shugabannin na da ‘yancin daukaka kara.
Dan takarar neman kujerar shugabanin FIFA Tokyo Sexwale na kasar Afrika ta kudu yace yanzu lokaci ne na Afrika ta karbe ragamar shugabancin FIFA domin tsabtace hukumar daga badakalar rashawa.
Sexwale yace babu dan Afrika da ya taba jagorantar FIFA a tsawon shekarunta 111. A cewarsa yanzu lokaci ya yi.
Sexwale dai na takara ne da Yarima Ali bin al Hussein na Jordan da sakataren kwallon Turai UEFA Gianni Infantino da shugaban kwallon a yankin Asiya Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa da kuma Champagne, tsohon sakataren FIFA.
Title :
FIFA ta dakatar da Blatter da Platini na tsawon shekaru 8
Description : Kwamitin tabbatar da’a da binciken rashawa da ta dabaibaiye hukumar FIFA ya dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini daga shiga sha’anin kw...
Rating :
5