Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kame tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, da kuma shugaban gidan talabijin na AIT a Nigeria, Raymond Dokpesi.
Wata majiya a hukumar ta EFCC ta tabbatar wa BBC cewa, kama Bafarawa da Dokpesi na da alaka da binciken da ake yi a kasar game da badakalar dala biliyan biyu da ake zargin an yi sama da fadi da su a ofishin tsohon mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.
Wani kwamiti da shugaban Nigeria ya kafa don bincika kudaden da aka kashe kan samar da makamai don yaki da Boko Haram a Nigeria ya ce ya gano an yi sama da fadi da kudaden da suka zarta dala biliyan biyu.
A don haka hukumar EFCC ke ci gaba da kama wadanda ake zargi da hannu a badakalar, wadanda suka hada da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki, da tsohon ministan kudi Bashir Yuguda, da sauransu.
Source BBC
Title :
EFCC Ta Kama Bafarawa Da Shugaban Tashar AIT
Description : Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kame tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahi...
Rating :
5