Hukumar Hana Harkalla Da Zamba Da Almundanar Kudade EFCC, ta rufe asusun ajiyar kudin tsohon dan ta’addar yankin Neja Delta, Tompolo a bisa zargin an karkatar da wasu makudan kudaden hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, NIMASA a cikin asusun nasa.
Idan ba a manta ba, a lokacin gwamnatin Jonathan ne aka ba Tompolo kwangilar kula da harkokinn tsaron tashoshin inda aka yi yarjejeniyar bilyoyin nairori domin gudanar da tsaro na tsawon shekara goma.
Dama kuma jama’a tun a lokacin sun koka da kwangilar ganin cewa akwai jami’an tsaro a kasa don haka bai halatta a ba wani tsohon dan ta’adda aikin tsaron tashoshin ruwa ba. Tun cikin makon da ya gabata ne dai EFCC ta cafke shugaban hukumar tare da wasu manyan mukarraban sa.
Title :
ECFF Ta Rike Asusun Ajiyar Kudin Tompoalo
Description : Hukumar Hana Harkalla Da Zamba Da Almundanar Kudade EFCC, ta rufe asusun ajiyar kudin tsohon dan ta’addar yankin Neja Delta, Tompolo a bisa...
Rating :
5