Dukkan Kalmomin yabo da kirari da godiya sun tabbata gareka Ya Allah.. Gashi cikin ikonka mun wayi gari tare da ni'imarka da lafiyarka da rufin asirinka da falalarka.
Ya Allah mu masu laifi ne, ka yafe mana..
Ya Allah mu masu rauni ne ka Qarfafemu.
Ya Allah mu Majinyata ne ka bamu lafiya.
Ya Allah mu matsaraita ne ka Suturtamu.
Ya Allah mu Mayunwata ne ka ciyar damu.
Ya Allah mu Matalauta ne ka azurtamu.
Ya Allah mu batattu ne ka Shiryar damu.
Ya Allah mu masu Qunci ne ka yaye mana.
Ya Allah mu Mawahalta ne ka saukaka mana.
Ya Allah mu mabukata ne ka Yalwata mana.
Ya Allah mu Makaskanta ne ka daukakamu.
Ya Allah yadda ka hadamu a Zauren Fiqhu muke kaunar Juna dominka, Ya Allah kasa wannan kaunar ta amfanemu aranar Alqiyamah.
Ya Allah ka amshi rokonmu, Kai ne Majibincin lamarinmu. Bamu da Matsera ko mafaka daga gareka sai awajenka.
Yi salati da aminci bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa tsarkaka adadin numfashin halittunka, Sau adadin kalmominka.. Ka dawwamar da Salatin da amincin agareshi gwargwadon dawwamar Ilahiyyarka.
Aaameeen.
Title :
Addu'ar Mu A Kullum
Description : Dukkan Kalmomin yabo da kirari da godiya sun tabbata gareka Ya Allah.. Gashi cikin ikonka mun wayi gari tare da ni'imarka da lafiyarka d...
Rating :
5