Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki zai ci gaba da zama a gidan kurkuku na Kuje dake Abuja har zuwa lokacin cimma yarjejeniyar bada belinsa.
Dasuki da mutane irin su tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda da Sagir Bafarawa da hukumar EFCC ke zariginsu da laifuka 22, an bada belin su ne a yau Litinin kan naira milyan 250 ga kowannen su, inda kuma aka bukaci su gabatar da mutane biyu da za su tsaya musu da kuma mika fasfo din su ga babban kotun na Abuja. Sannan kuma kotun ta dage sauraren karar zuwa 2 da 3 na watan Fabrairu, 2016.
Title :
Dasuki Na Ci Gaba Da Zama A Gidan Kurkukun Kuje
Description : Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki zai ci gaba da zama a gidan kurkuku na Kuje dake Abuja har zuwa...
Rating :
5