Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa duk da cewa a lokacin yakin neman zabe bai goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, amma ya bayyana cewa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ci zaben 2015 da kasar ba za ta kai shekaru hudu ba za ta wargajewa.
Farfesa Soyinka ya kara da cewa sata da almundahana da dukiyar kasa da sauran laifuka makamantan haka su suka dabaibaye gwamnatin da ta shude.
Soyinka ya bayyana haka ne a wani shiri da gidan talabijin na Channels ya gabatar a jiya.
Title :
Da Jonatha Ya Ci Zaben 2015, Da Nijeriya Ta Wargaje- Farfesa Wole Soyinka
Description : Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa duk da cewa a lokacin yakin neman zabe bai goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Bu...
Rating :
5