DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
An bayyana rashin gamsuwa da kuma damuwa akan kalaman da rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta bakin shugabanta Solomon Arase tayi akan batun ganin Malam Zakzaky, inda tace babu mai ikon ganinsa sai idan sun samu izini daga sama.
Wani babban na hannun daman Zakzaky kuma sanannen mai wa'azin addinin Kirista a tarayyar Nijeriya Pastor Yohanna Buru, yayi wannan koken a yayin wata tattaunawa da RARIYA a garin Kaduna.
Pastor Buru ya kara da cewar kalaman babban baturen 'yan sanda na kasa Arase, suna kama da wani yarfe ga shugaban kasa Buhari, wato ya zamana cewar su sun wanke kansu sannan sun hada shugaban kasa da masoyan Malam Zakzaky rigima.
Sanannen kiristan ya cigaba da cewar kamata yayi rundunar 'yan sanda ta bada dama ga Almajiran Zakzaky su gana dashi ba tare da wata togaciya ba, amma muddin ya zamana cewar sai shugaban kasane zai bada izinin ganinshi, to yana kira da babbar murya ga shugaban kasa ya amince mishi su gana da Zakzaky.
Babban Paston wanda ya samar da masallaci a cikin gidanshi domin musulmai su rinka sallah a ciki, ya kuma soki lamirin kungiyar gwamnonin arewacin kasarnan, dangane da yadda suke ko in kula da malaman addinai a yankin, sai idan al'amari ya lalace sannan su fito suna kunfar baki. Dangane da batun shawarar da gwamnonin arewa suka yanke na hana dukkanin wanin gangami na kungiyoyin addinai ba tare da izini ba a yankin, Pastor Buru yace matakin yanada kyau, matukar gwamnonin sunada kyakkyawar niyya a zukatansu.
Pastor Yohanna Buru, wanda aka tabbatar da cewa, tarihin Zakzaky ba zai cika ba sai idan an sanyo shi a ciki, ya yi kira ga Almajiran Zakzaky da cewar su taka a sannu dangane da yunkurin Muzaharori da suke shirin aiwatarwa na sakin Zakzaky, su zuba ido su ga ikon Ubangiji.
Title :
Da Akwai Lauje Cikin Nadi, Akan Batun Tsare Zakzaky, Inji Pastor Yohanna Buru.
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA An bayyana rashin gamsuwa da kuma damuwa akan kalaman da rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta bakin shugabant...
Rating :
5