Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta kori kocinta, Jose Mourinhou daga aiki watanni bakwai bayan ya jagorance ta wajen lashe kofin Gasar Premier.
Dan kasar Portugal din, mai shekaru 52 a duniya, yana tsaka da yin wa'adinsa na biyu ne a kungiyar, bayan ya karbi ragamar horas da 'yan wasanta a shekarar 2013.
Kungiyar Chelsea ta kammala kakar wasan Premier da ta wuce da maki takwas kan kungiyar da ke biye mata, kuma ta lashe kofin League, sai dai a kakar wasa ta bana kungiyar ta shiga halin tsaka mai wuya, inda ta yi asarar maki tara a cikin wasanni 16 da ta buga.
Wasa na karshe da Mourinho ya jagoranta shi ne wanda kungiyar Leicester City ta doke su da ci 2-1.
Ana sa ran za a maye gurbinsa da ko dai Pep Guardiola ko Guus Hiddink ko Brendan Rodgers ko kuma Juande Ramos.
Title :
Chelsea ta kori Jose Mourinho
Description : Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta kori kocinta, Jose Mourinhou daga aiki watanni bakwai bayan ya jagorance ta wajen lashe kofin Gasar Premie...
Rating :
5