Tsoffin shugabannin kasa guda 11 da mataimakansu za su kasafta naira bilyan 2.3 a kasafin kudi na 2016.
Jawabin na kunshe ne cikin takardar da shugaban kasa ya karanto a gaban majalisa kan kasafin 2016.
Tsoffin shugabbannin kasar sun hada da Janar Yakubu Gowon, Alhaji Shehu Shagari, Janar Ibrahim Babangida, Janar Abdulsalam Abubakar, Janar Olusegun Obasanjo, da Goodluck Jonathan. Sai kuma tsoffin mataimakan shugaban kasa, Alex Ekwueme, Janar Oladipupo Diya, Alhaji Abubakar Atiku da Alhaji Namadi Sambo.
Kamar yadda doka ta tanadar, kowanne daga cikin tsoffin shugabannin kasar zai dinga karbar naira dubu 350 a duk wata, yayin da su kuma mataimakan shugaban kasa za su dinga karbar naira dubu 250 a duk wata domin biyan bukatunsu.
Title :
Buhari Ya Warewa Tsoffin Shugabannin Kasa Naira Bilyan 2.3 A Sabuwar Shekara
Description : Tsoffin shugabannin kasa guda 11 da mataimakansu za su kasafta naira bilyan 2.3 a kasafin kudi na 2016. Jawabin na kunshe ne cikin takarda...
Rating :
5