Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa 'yan kasar hakuri saboda matsananciyar matsalar man fetur din da suke fama da ita.
Shugaba Buhari ya nemi gafara ne a lokacin da yake gabatar da kudurin kasafin kudin shekara ta 2016 a gaban majalisar dokokin kasar.
Shugaban na Najeriya ya ce ya bayar da umarni ga hukumar da ke kayyade farashin man fetur da ta sake duba yadda take kayyade farashin man, yana mai umartar ta da ta tabbatar a yanzu farashin bai wuce N87 kan kowacce lita daya ba.
Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne na Naira tiriliyan 6.08 a kan kowacce gangar danyen man fetur $38 da kuma N190 kan kowacce dalar Amurka.
Fannin ilimi ne ya samu kaso mafi tsoka
An ware N396bn domin bai wa fannin ilimi, yayin da aka ware N296bn kan kiwon lafiya, sannan aka ware N294bn ga fannin samar da tsaro.
Haka kuma shugaba Buhari ya ce za a warre kashi talatin cikin dari na kasafin kudin domin gudanar da manyan ayyuka, sannan aka ware kashi 70 cikin dari domin yin ayyukan yau-da-kullum.
Shugaban kasar ta Najeriya ya sha alwashin kwato dukkan kudaden kasar da aka sace, ko da kuwa hakan zai kai shi har karshen wa'adin mulkinsa.
Title :
Buhari ya bayar da hakuri kan matsalar fetur
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa 'yan kasar hakuri saboda matsananciyar matsalar man fetur din da suke fama da ita. Shugaba...
Rating :
5