Wani Liyutanal Janar na sojojin Nijeriya ya rasa ransa sakamakon farmakin da 'yan Boko Haram suka kaiwa wata tawagar sojoji da suke kan hanyar dawowa garin Bama bayan wata ziyara da suka kai garin Maiduguri.
Duk da cewa cikakken rahoto game da harin bai gama fita ba a daidai lokacin hada wannan rahoto, wata majiya dake kusanci da dakarun sojojin ta bayyana cewa tawagar sojojin sun rage gudu ne a lokacin da suka iso wurin da ke da gargada a titin, inda a nan ne 'yan bindigan suka bude musu wuta.
Rahotanni sun nuna cewa sojoji da dama sun samu rauni sakamakon harbin bindiga a yayin farmakin, sannan kuma motocin su sun nakasa.
'Yan bindigan sun gudanar da farmakin ne a daidai babban titin Bama da Konduga da ke kusa da dajin Sambisa.
Title :
Boko Haram Sun Kashe Liyutanal Kanal Din Sojojin Nijeriya
Description : Wani Liyutanal Janar na sojojin Nijeriya ya rasa ransa sakamakon farmakin da 'yan Boko Haram suka kaiwa wata tawagar sojoji da suke kan...
Rating :
5