Kisan Kiyashi Kan 'Yan Shi'a A Garin Zariya Tare Da Bisine Su A Wagegen Rami
Tsohon shugaban kungiyar kare hakkin bil-Adama a Nigeriya ya bada labarin cewa akwai tabbacin sojojin gwamnatin Nigeriya sun haka babban rami tare da bisine tarin mutanen da suka kashe a Zariya.
Tsohon shugaban kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Nigeriya ta National Human Rights Commission Dr Chidi Odinkalu ya sanar da cewa; A matakin da sojojin gwamnatin Nigeriya suka dauka na kokarin boye yawan ‘yan shi’ar da suka kashe a garin Zariya da ke jihar Kaduna sun haka babban rami tare da bisine gawawwakin jama’a a ciki.
Dr Chidi Odinkalu ya kara da cewa; Sojojin gwamnatin Nigeriya sun kashe daruruwan ‘yan shi’a, kai wasu rahotonni ma suna cewa sun haura 1000, don haka kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suna kira ga gwamnatin kasar da ta sanar da su wajen da aka turbude gawawwakin tare da gano bayyana sunayen jami’an da suka bada wannan umurni na kokarin boye jama’ar da aka kashe.
Tsohon shugaban kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Nigeriya Dr Chidi Odinkalu ya bayyana cewa; A bayan kai harin ta’addancin birnin Paris na kasar Faransa shugaban kasar Nigeriya Muhammadu Bukhari yana daga cikin sahun gaba na yin Allah wadai da harin, amma ya kama baki ya yi shiru kan kisan kiyashin da aka yi a kasarsa tare da nuna halin ko-in kula kan lamarin.
Title :
Bisine Daruruwan 'Yan Shi'a A Wagegen Rami Bayan Kisan Gillar Da Aka Yi Musu A Zariya
Description : Kisan Kiyashi Kan 'Yan Shi'a A Garin Zariya Tare Da Bisine Su A Wagegen Rami Tsohon shugaban kungiyar kare hakkin bil-Adama a Niger...
Rating :
5