Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abinda gwamnatin kasar nan a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari. Domin kuwa a cewar ita sabuwar gwamnatin ta Buhari, sun sami kasar a gurgunce saboda illar da wawaso da babakere ya yi mata ya hana kasar motsi.
An sami badakalar da ta taso wacce ke da alaka da matsalar al’mundahana da dukiyar kasa wacce ta ja har aka cafke Kanar Sambo Dasuki mai ritaya kuma tsohon mashawarcin Shugaban Najeriya zamanin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da ya sauka bayan kayin da Shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari yayi masa.
Wannan kamu na Sambo ya zame wata allura da ta tono garma har ta giggirbi manyan kasar nan da dama, ciki har da tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa. Inda shi ma wannan guguwar ta kwasa da shi har gaban hukumar EFCC masu yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Bayan kwashe kwanaki a hannunsu aka rankaya kotu a kasar, daga baya aka bada belinsu.
An ta yama didi da maganar cewa shima Bafarawa ya karbi makudan kudaden da suka kai Miliyan Dubu Hudu Da Dari Shida, da aka ce yace ya karba ne don rabawa Malamai a kokarin samun nasarar zarcewar tsohuwar gwamnatin kasar.
Title :
Batun Kudi Bai Taba Shiga Tsakanina Da Dasuki Ba, Inji Bafarawa
Description : Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abinda gwamnatin kasar nan a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari. Domin kuwa a cewar ita ...
Rating :
5