Yan Nigeria na ci gaba maida martani a kan matakin wasu bankunan kasar na dakatar da cire kudi da katin ATM a kasashen waje.
Wasu bankunan sun ce daga ranar 1 ga watan Junairun 2016, duk wanda ke da asusun ajiya a wasu bankunan Nigeria, ba zai iya cire kudansa ba a kasashen waje kamar yadda aka saba.
Wasu daga cikin 'yan kasar musamman dalibai a kasashen waje na ganin cewar matakin zai jefa su cikin tsaka mai wuya.
Daya daga cikin bankunan na cewar karancin kudaden kasar waje ne ya janyo suka dauki wannan mataki.
A yanzu haka dai darajar Naira na kara faduwa idan aka kwatanta da dallar Amurka sannan kuma faduwar farashin man fetur ta kara janyo karancin dalar Amurka a Nigeria.
Title :
ATM din Nigeria zai daina aiki a kasar waje
Description : Yan Nigeria na ci gaba maida martani a kan matakin wasu bankunan kasar na dakatar da cire kudi da katin ATM a kasashen waje. Wasu bankunan ...
Rating :
5