Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da Yahaya Bello na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi.
Yahaya Bello wanda ya maye gurbin marigayi Abubakar Audu a takarar zaben, ya doke gwamna mai ci na Jami'yyar PDP Captain Idris Wada wanda ya ke kokarin komawa kujera a karo na biyu.
A yayin da yake sanar da sakamakon zaben Farfesa Emmanuel Kucha babban jami'in zaben ya ce dan takarar jam'iyyar APC ya samu kuri'u 247,752 yayin da dan takarar jam'iyyar PDP ya samu 204,877
Wannan shi ya kawo karshen zaben gwamnan wanda aka soma a ranar 21 ga Nuwamba a inda hukumar ta ce bai kammalu ba.
Sakamako daga kananan hukumomi 21 na jihar a watan Nuwamba ya nuna cewa marigayi Abubakar Audu na APC na kan gaba da kuri'u 240,867 yayin da Captain Wada na PDP na biye da kuri'u 199,514 'yar tazarar da ta gaza yawan kuri'un da aka soke 49,953
Zaben na Kogi ya kafa tarihi kasancewasa na farko a inda jam'iyya ta sauya dan takararta a tsakiyar zabe.
Title :
APC Ta Lashe Zaben Jihar Kogi
Description : Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da Yahaya Bello na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kog...
Rating :
5