Yayin da bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara ke karatowa, a Najeriya matsalar karancin man fetur yana cigaba da zama wani babban kalubale da yake damun kasar
Kamar sauran jihohin kasar a jihohin Adamawa da Taraba dogayen layuka ake gani a wasu gidajen man dake sayarwa.
Jama'a na shafe awanni masu yawa kafin su sami man.Wasu masu ababen hawa sun ce matsalar man fetur ta zama kamar abun al'ajabi. Wasu ma wuni su keyi suna kan layi kuma wani zubin daga karshe ma sai a tashi babu man. Tun da sassafe mutane ke baro ayyukansu su shiga layin neman sayen mai.
Karancin man ka iya shafar bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara.Wani malami a kwalajin kimiya da fasaha dake Yola yace ba bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara ba kawai zai shafa ba har ma da ayyukan gwamnati da kasuwanci. Ma'aikata da ya kamata suna bakin aikinsu sai su yi kwana biyu uku suna kan layin mai.
Amma a yayin da ake fama da karancin mai su kuwa masu sayar dashi ta kasuwar bayan fage ko "black market" kakarsu ce ta yanke saka domin suna cin karensu babu babbaka sai dai sun ce da jami'an tsaro su ke raba ribar wadanda sukan zo karbar na goro a wurinsu kullum.
Title :
Ana Ci Gaba Da Karancin Man Fetur
Description : Yayin da bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara ke karatowa, a Najeriya matsalar karancin man fetur yana cigaba da zama wani babban kal...
Rating :
5