Wasu ‘yan bindiga sun sace kanwar gwamnan jihar Bayelsa Nancy Dickson kamar yadda hukumar ‘yan sanda suka tabbatar a jiya lahadi.
Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Bayelsa Asinim Butswat, ya bayyanawa manema labarai cewa, an sace Nancy Dickson mai kimanin shekaru 26 a shagonta da ke unguwar Okaka a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.
Butswat, ya kara da cewa, yan bindigan sun yi awan gaba da Nancy ne a ranar Asabar da misalin karfe 2:50 na rana wanda har yanzu babu labarin inda ta ke.
Title :
An Sace Kanwar Gwamnan Bayelsa
Description : Wasu ‘yan bindiga sun sace kanwar gwamnan jihar Bayelsa Nancy Dickson kamar yadda hukumar ‘yan sanda suka tabbatar a jiya lahadi. Kakakin h...
Rating :
5