Kasar Beunei dake yankin Asia wadda ta haramta gudanar da duk wwni addini a kasar bayan Musulunci, ta kuma haramta gudanar da shagulgulan Kirsimeti, inda ta yi barazanar yanke hukuncin zaman shekara biyar a gidan wakafi ga duk wanda aka kama da saba dokar a cikin kasar.
Sauran wasu abunuwan da Sarki Hassanal Bolkiah ya haramta sun hada da wake waken Kirsimeti sakon gaisuwar Kirsimeti da makamantan haka.
An baiwa Kiristocin kasar damar gudanar da shagulgulan Kirsimetin ne a iya mazaunin su ba tare da sun shiga hakkin Musulman kasar ba, wanda sune suka fi rinjaye.
A gefe daya kuma, ita ma kasar Somalia ta samar da doka makamancin haka ga Kiristocin kasar.
Source Rariya
Title :
An Haramta Shagulgulan Kiristimeti A Kasashen Brunai Da Somalia
Description : Kasar Beunei dake yankin Asia wadda ta haramta gudanar da duk wwni addini a kasar bayan Musulunci, ta kuma haramta gudanar da shagulgulan K...
Rating :
5