Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta ceto mutum 210 da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a wasu kauyuka hudu da ke jihar Borno.
Rundunar ta ce sojojinta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram biyar, kuma sun kwace makamai a arangamar da suka yi a garin Furkati da ke karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Usman Sani Kukasheka, ya ce sojoji sun kwato wadannan mutane bayan bayanan da suka samu cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa kauyukan hari.
A cewarsa, mayakan sun dinga garkuwa da mutane a kauyukan Ejilihe da Bulagaije-Lari da Bulaigaije Adamde da kuma Ajiri wadanda suka hada da tsoffafi da mata da kuma yara.
Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce tuni aka turo da mutanen zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira.
Title :
An Ceto Mutane 210 Daga Hannun Boko Haram
Description : Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta ceto mutum 210 da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a wasu kauyuka hudu da ke jihar...
Rating :
5