Jami’an tsaro sun cafke kimanin mutane 20, a karamar Amuwo Odofin, dake Lagos, da ake zargi da satar mai ta hanyar fasa bututun man.
Hukumar dake kula da cinikayyar albarkatun Mai ta ce an kama mutane ne a lokacin da jami’an tsaro ke sintiri akan hanyar da bututun Man ya ratsa, a tsakanin Atlas Cove da Mosimi.
Shugabar hukumar Mrs. Esther Nnamdi Ogbue, ta ce a makonin 2, da suka gabata anyi nasarar dakile satar Mai, inda aka samu kwato motoci da jarkoki da Janaretoci daga hannun maso aika wanna ta’asa na satar Mai da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Ta kara da cewa wadanda aka cafke za’a tabbatar da ganin cewa sun gurfana a gaba kuliya domin ya kasance ishara ga sauran masu aika ta wadannan mutane.
Title :
An Cafke Wasu Masu Satar Mai
Description : Jami’an tsaro sun cafke kimanin mutane 20, a karamar Amuwo Odofin, dake Lagos, da ake zargi da satar mai ta hanyar fasa bututun man. Hukum...
Rating :
5