Yan Sanda na masamman masu yaki da masu farshi da makaimi na rundunar jihar Ogun sun cafke wani Musiliu Otun, wanda yake ajiyewa ‘yan fashi makamansu kuma ya kasance Bokan su.
Da yake tabbatar da lamarin kakakin rundunar ‘yan Sanda ta jihar Ogun, Muyiwa Adejobi, ya ce bincike kawo yanzu ya nuna cewa shi wannan Boka ya taka rawa a fashi da dama a jihar abinda yayi sanadiyar cafke shi.
Kakakin ya ce an kama shi wanna Boka ne a yankin Sagamu kuma an sameshi da makamai da layu da sauran tsubbuce tsubbuce.
Kakakin ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Abdulmajid Ali, ya bada umarnin cewa a gudanar da binciken da ya kamata, ya kuma ce rundunar zata yin duk abunda ya dace domin kiyaye lafiya da dukiyoyin jama’ar jihar.
A wani labari kuma rudunar ta cafke wani Kabiru Soyemi, a bisa zargin fashi da makami da harkokin kungiyr asiri.
Runduinar tace wandanda ke hanu a yanzu na taimakawa hukumomin ‘yan Sanda wajen bincikensu.
Title :
An Cafke Wani Boka Mai Taimakawa 'Yan Fashi Da Makami
Description : Yan Sanda na masamman masu yaki da masu farshi da makaimi na rundunar jihar Ogun sun cafke wani Musiliu Otun, wanda yake ajiyewa ‘yan fashi ...
Rating :
5