Na karasa kai wayar kunnena yalwataccen murmushi na tashi daga fuskata, sai dai tayi saurin canjawa daga annuri zuwa rashin fahimta sanda naji muryar dana tbbtr ba tashi bace.
Idan har a yadda muka fahimta dai-daine Ga alama kece matar me wayar nan ko??
Ckn y‘an sakannin da yayi na maganar 2n kafin yakai karshe fuskata ta rikide daga yadda take a baya zuwa mummunan yanayin daya wuce misaltawa nayi saurin cewa “Eh...eh nice la..fiya meye ya faru??“
ka2war muryar tamkar ana buga diro dake magana tayi shiru zuwa can tace “To kiyi gaggawar zuwa asibitin SABO TAIWO HOSPITAL mijinki ya samu mummunan accident...“
Iya abnd kunnuwana suka iya jiye min kenan suka dauke dif ma‘ana suka daina jin komai, wani duhu ya ziyarci idanuna na daina ganin inda nake tsaye ma bare nesa. Kaina kuwa wata irin juyawa ya fara yi kwatankwacin yadda belt din inji ke juyawa sanda yake aiki, wani gumi me zafi ya fara ketowa ta ko‘ina daga jikina tamkar an watsa min ruwan zafi.
(wani yasaman yacemin wai ina tsalleke..to ni ban tsallake duk wanda be gani haq qarke to se ya koma ta opera zegani har inda mu ka tsaya..)A tsaye nake na kasa gaba na kasa baya, a takaice dai gaba daya na dauke wuta, ni kaina banyi yunkurin motsawa ba don nasan faduwa ce zata biyo baya saima mika hannuna da nake yi wai ko zanji bango na dafa amma babu. Na shiga yanayi mafi muni 2nda uwata ta haifeni yau sanadin MUMMUNAN ALBISHIR!!
Bansan sanda wayar ma dake hannuna ta subuce zuwa kasa ba, tana dira kuwa ta tarwatse komai nata ya rabu da dan uwansa, na dade a tsaye tamkar gunki dafe da kaina dake juyawa.
Zuwa jimawa kadan dana ji dan dama-dama na yunkura da karfi daga inda nake tsaye wani jiri ya kwasheni ta gefe nayi kasa sai dai bisa sa‘a jina kawai na fado akan kujera, na dunkule kaina na fashe da kuka hawaye na zuba tamkar ruwan sama.
Zaiyi wuya in ban rasa faruk ba. 2nanin da nayi kenan wanda yasa nayi gaggawar mikewa duk da ban gama dawowa dai-dai ba na jawo mayafina, takalmina da mukullin motar faruk duk na rikesu a hannuna nayo waje da gudu.
Banma yi yunkurin tsaida kukan da nakeyi ba don nasan bame yiwuwar tsayawa bane.
ganin a yanayin dana fito yasa salih tasowa tare da tambayar “hajiya lfy??
ya na ganki haka??
me ya faru kike kuka kuma??
Na daga baki dakyar nace “Faruk ne.. sunyi accident yanzu haka suna...asibiti...“
Nakai karshen maganar dakyar.
Subhanallahi!! Accident??
shima ya fada a gigice, hankalinsa ya tashi ma2ka.
Yayi saurin amsar mukullin dake hannuna ya bude min kofar motar, muna shiga ya juyar da ita muka fice.
Duk da gudun da salih keyi iya krfnsa amma na raina gudun ji nake kmr na sauka na ruga da gudu, kuka kawai nake rusawa 2n salih na bani hakuri har ya gaji ya daina.
Muna isowa harabar asibitin kukana ya karu 2n kafin ya gama tsayawa nayi ready na sauka, yana tsayawa nayi yunkurin fita yayi saurin dakatar dani da fadin “hajiya kiyi hakuri ki rage kukan nan don Allah ki samu nutsuwa ko yayane, dubi yadda kike fa!!
Nabi mayafina da takalmina wadanda duk suke rike a hannuna nabi shi da kallo kawai na saki takalmin zuwa kasa na zirashi ckn kafata na yafa mayafin akan kafata kawai nayo waje nayi saurin tsayawa sakamakon motar dana gani a nesa kadan dani na ganeta motar tasin da faruk yahau ce, gaba daya tayi raga-raga lallai ba karamin accident bane.
Nan fa na sake rudewa da firgici me tsananin, ‘IHHH!!!! bakina ya furta dai-dai sanda hakorana suka fara karo na sama na dukan na kasa ji kake KAF! KAF! KAF! jikina yadau tsima.
nasan zaiyi wuya wanda ke ckn motar nan ya fita da rai, na juya da gudu izuwa ckn asibitin bangaren Emergency na nufa don nasan bazai wuce can ba, 2n kafin na karasa naga an fito da wani daga daki bisa irin gadon nan da ake 2rawa an lullube jikinsa alamun ya mu2.
kawai ji nayi kafafuna sun dakata, SHIKENAN!! ya mutu!!
kukana ya canja salo, da sauri na tari gaban wadanda ke 2ra dan siririn gadon na dire a gabansa tare da bude mayafin dake rufe da fuskarsa.
Nadan yi baya a zaune KAI! ba faruk bane!! na ganeshi direban tasin ne.
Nayi wata juyawa a haka na mike tsaye da gudu na doshi dayan dakin dake kusa da wanda naga an fito da wancan.
Kai tsaye na fada da yake dakin nada zurfi zarcewa nayi zuwa tsakiyarsa, tfyt tayi saurin cnjw na koma tfy a hankali sabanin gudun da nake yi a baya.
Har na karaso gbn gadon da yake kwance, kwance yake idonsa a rufe tamkar meyin barci gaba dayan kansa na nade da farin bandeji, hannunsa dama kafarsa.
Numfashinsa na hawa da sauka a hankali, y‘ar farar kyakykyawar fuskarsa na klln sama.
Na tsaya akan gadon nasa na zuba masa ido da yanayin da yake ciki, nabi pipe na ledar karin jinin dake jone a jikinsa da kallo sama inda take rataye.
Wasu hawaye da suka banbanta da nadaa suka zubo min, Bai mutu ba.
Abinda na baiwa kaina tbbs kenan.
Na cake gwiwoyina a kasa na dora kaina bisa gadon gefensa kadan na zarce da kuka me tsanani, wanda duk wanda yaji sai ya tausaya min.
Na jima a haka ko sau daya ban dago kai ba, ji kawai nayi an dafa bayana a hnkl na dago kai muka hada ido da wata siririyar farar nurse dake sanye da fararen kaya, tayi murmushi tace “am sorry dan matsa kadan zan cire masa wannan ledar.
Na bita da kll da jajayen idanuna kawai na mike wani jiri yaja ni zan fadi nurse din ta taro ni da fadin “hankali zaki fadi fa.“
Na lallaba na zauna a kujerar dake gaf da gadonsa na kwantar da kaina a jkn bango hawaye suka cgb da sintiri a kuma2na.
Nurse din ta cire ledar jinin ta jona masa ledar karin ruwa, tadan tako kmr zata wuce sai kuma ta tsaya ta dubeni tace “kiyi hakuri kinji shi ai nashi yazo da sauki ma2ka, karki damu da yawa.“
Takai karshen maganar tare da dafa kafata ta wuce.
hmm... wane kwantar min da hankali ma zata iya yi??
Tayaya hankalina zai kwanta da wannan bala‘in??
Daga wannan sai wannan, murna ta koma ciki kenan takaici yaci uban nadaa.
Wannan wace irin KADDARA ce?? wane irin bala‘i ne??
yaushene zamuyi rayuwa kmr kowa??
ire-iren 2nanin daya mamaye kwakwalwata kenan.
******* ****
Tunane-tunanen nata karo a ckn kwakwalwata, a haka dai naci gaba da zama a kujerar dake gaf da faruk na zuba tagumi tare da kurawa faruk idanu, ba yanayin da yake ciki yanzu nake kll ba amma ainihinsa nake kallo.
kyakykyawar dariyarsa, ingantaccen murmushinsa, da yalwatacciyar fa‘ararsa.
Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Ko a lbr ban taba jin wadanda masifa ta taso su a gaba kmr mu ba, daga wannan sai wannan??
KADDARA!!!
KADDARA!!!
KADDARA!!! itace kawai kalmar dake min yawo a zuciyata.
Domin idan tazo ba yadda aka iya sai dai ayi hakuri a rungumeta, ji nayi kawai dama banma mike nayi tafiya ba faruk ya fita yayi tafiyarsa tuntuni da duk haka bata faru ba. Amma ya muka iya???
Sai da yamma ta farayi sosai sannan ma nayi wani tunanin sanar da wani halin da ake ciki, sai sannan na 2na inda na jefar da wayata can a gida lkcn dana rude sanda lbrn abnd ya faru ga faruk ya isarmin.
Wayar wannan nurse din wadda itace keta zarya akan faruk na ara na kira mufida da nazir bbn abokin faruk da yake umminsa ta tafi umara banyi yunkurin kiranta ba, sai kuma momi dana kira daga karshe.
Momi naji ta rafka salati tare da tambayar “subhanallahi!!
Wane asibitin??“
muna SABO TAIWO HOSPITAL!!
da dan AL‘AJABI ta tambayeni “waye ya daukeki ya kaiki can??“
Bata san halin da ake ciki ba, bata san cewa na dawo dai-dai ba zatonta har yanzu ni gurguwa ce.
Bata samu wata amsa ba saima rushewa dana sake yi da kuka na janye wayar daga kunnena a hnkl, ji nake kmr kaina zai fashe sbd zafi da yayi min.
Mufida ce ta fara zuwa kusan karfe biyar na yammaci lkcn, hankalinta ya tashi ma2ka amma da yake tana da nutsuwa a dan lkc ta fara rarrashina da kalamai masu dadi da saka nutsuwa sai dai ina!!
bata sami kaina ba saima wani kuka daya kara turnuke ni.
Mufida ta rasa yadda zatai dani tadan rike kafaduna tare da cewa “HUMAIRA!! wai me kike so ki zama ne??
Ke ba zaki iya jurar kaddara ba kenan??
Ko kina zaton Haka kawai Allah zai bar bawansa ba jarraba ba.
kuma gsky ta fada fa 2nda faruk dai ba mutuwa yayi ba amma yakamata tasan ba yadda za‘ai koda ciwon kai ya sami faruk hankalina ya kwanta bare hali irin wannan.
daga karshe dai na roketa alfarma da taje gd ta dauko mana wasu abubuwan da zamu bukata, tako mike tare da tambayata ina mukullayen gdn??
Na dan kauda kaina kawai a raina nace gsky wannan ta samu matsala, a ina na sami nutsuwar daukar wani mukulli??
Zuwa jimawa na dubeta da shakakkiyar muryata nace “kije kawai komai a bude yake.“
Ta dan bini da kll kawai tare da girgiza kai cike da tausayawa ta juya ta fice.
Naja kujerata izuwa fuskantar faruk nayi tagumi kawai, ji nake inama nice a kwance bashi ba!!
Ina ma ni masifa ta riska bashi ba!!
ina ma nice hakan ta faru dani bashi ba!!
Sai byn wasu lkt mufida ta dawo, nazir da abkn faruk su uku suka zo, momi ma ba shiri ta bazamo.
Likitan dake kula da faruk ma yayi bayani gamsashshe daya kwantar min da hankali ma2ka, a cewarsa ‘faruk bai sami wata matsala ba saboda kaf ilahirin jikinsa kalau yake iya kansa ne kawai yadan sami buguwa da karfen motar da sukai hatsari akanta shine ma dalilin saka bandejin dake kansa sbd suna tsammanin ko akwai inda ya fashe kuma babu ma hkn yasa bayan wani lokaci suka cire, akwai yiwuwar farfadowarsa nan da wayewar gari.‘
Hakan yasa nadan ji sanyi a raina sosai, tbbs abin yazo da sauki sosai nima na yarda da hakan.
Gefe guda momi dasu nazir AL‘AJABI ya ma2kar turnikesu ganin yadda nake taka kafata tamkar bani ba, na fahimci momi nason tambayata shiru dai kawai tayi.
Sanda dare ya tsala sannan ne duk suka tafi ya rage ni da faruk kawai sai kayayyakinmu daga gefe guda kuma y‘ar hayaniya na tasowa daga waje da yake dakin da muke na musamman ne ba kowa a cknsa sai kuma nurses dake ta kaiwa da komowa don ganin komai ya tafi dai-dai.
Na koma daga can gefen gadonsa na shimfida darduma na fara sallolin nafil-fili da addu‘o‘in samun sauki ga abin alfaharina guda daya tak a duniya, Allah yasa yadda muke tsammani ya zama haka ne.
Addu‘ar dana kwana inayi kenan don ban iya runtsawa ba a daren.
*WASHE GARI*
misalin karfe 10:00 na safiyar ina zaune a kasa bisa shimfidar da nayi nayi tagumi kawai kusan hankalina baya jikina na tafi duniyar 2nani, gwauron numfashin da aka kawo yasa ni dawowa hayyacina na dago kai da sauri na dubi inda sautin ya fito.
FARUK ya farfado!!
abnd na fara fada a zuciyata kenan, nayi zumbur na mike na zauna a gefensa.
fuskata tadan fara saki sanda na tbbtr da abnd nake zato, a hnkl idanunsa suka bude sosai ya yunkura ya mike zaune wani murmushi hade da hawaye suka ziyarceni nadan kawo gwauron numfashi tare da hada hannuna ckn nasa.
Yace “HUMAIRA“ na amsa da “na‘am FARUK!!“
Meya faru dani haka ne??
A ina nake??
kina ina ne ba fitila a inda muke ne?? Nayi saurin sakin hannunsa kirjina ya buga da karfi, kaina ya sara tamkar kwakwalwata zata rushe.
Ba kaganni bane??
Rikici kenan...anya kuwa..
Komeyasameshi..???