Hakika abin nan da yake faruwa a Zaria, ba Qaramin abin bakin ciki bane ga dukkan al'ummar Nigeria. Musamman Mazauna arewacin Nigeria, Musamman ma Mu Musulmai.
Ni ba 'dan Shi'ah bane, Kuma bani da wata dangantaka dasu acikin abinda suke kudurcewa ko suke furtawa wanda ya sa'ba ma Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww).
Amma bisa hakikanin Gaskiya an zaluncesu, anyi musu kisan gilla ko kuma Kusan kiyashi kusan wanda ba'a ta'ba yin irinsa ba atarihin Qasar nan.
Ko acikin rikicin Boko Haram babu inda aka ta'ba rabarbashe rayukan Mutane masu yawa acikin lokaci Qankani irin wannan.
Nayi mamaki da naga wasu Musamman masu danganta kansu da wata Qungiya sun fito suna nuna murnarsu da goyon bayansu bisa Kisan gillar da ake yiwa 'Yan shi'ah.
Wannan ba daidai bane. Kuma ya saba ma Ainahin koyarwar Manzon Allah (saww) domin kuwa shi Manzon Allah (saww) ya nuna mana cewar shi Musulunci Kowanne mai rai mutum ko dabba yana da Daraja da Mutunci awajen Allah.
Ballantana 'Dan Adam wanda Allah ya fifitashi sama da dukkan Halittunsa. Kamar yadda ya fada acikin Alqur'ani :
"KUMA HAKIKA MUN GIRMAMA 'YA'YAN ADAMU KUMA MUN DAUKESU AKAN TUDU DA KUMA TEKU, KUMA MUN AZURTASU DAGA TSARKAKAN ABUBUWA, KUMA MUN FIFITASU, MUTUKAR FIFITAWA BISA MAFIYA YAWAN ABINDA MUKA HALITTA".
Don haka 'lallai wannan abinda yake faruwa lallai koda acikin Enugu ne ko Onitsha bai kamata Musulmi yayi murna dashi ba.
Idan kana murna ne wai Saboda Qiyayyar dake tsakanin Qungiyarka da shi'a, To kar ka manta cewar abin nan zai shafi Mafiya yawan mutanen da basu yin shi'ar ma.
Akwai Matan aure, Akwai kuma Tsofaffi wadanda basu yin shi'ar. Amma watakil 'dansu yana yinta. Watakil Shi yake ciyar dasu, shi yake biya musu kudin gidan haya.... To yanzu Sojojin Gwamnati sun kasheshi.. Shin ta yaya iyayen nan nasa zasu iya rike kansu??
Bayan wannan ku dubi kusancin Zaria da sauran biranen tsakiyar arewacin Nigeria kamar su Kano, Kaduna, Funtua, Jos, Abuja, etc. Kunga idan rikicin yaci gaba (bamu fatan hakan) amma abun sai ya shafi Duk wadannan Biranen da na lissafa, Harma da Kauyukan da ba zasu lissafu ba.
Ya kamat duk Musilmi mai hankali yayi addu'a da Fatan Allah shi kawo Qarshen wannan bala'in. Aaameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP
zaku iya tura mana naku labarai ta shafin na Facebook
Title :
Abin Kaicho, Abin Takaici
Description : Hakika abin nan da yake faruwa a Zaria, ba Qaramin abin bakin ciki bane ga dukkan al'ummar Nigeria. Musamman Mazauna arewacin Nigeria, M...
Rating :
5