Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari ta waya, inda ya bukaci masaniya kan arangamar da ta auku tsakanin sojojin kasar da mabiya mazhabar Shi’a wadda ta yi sanadiyar mutuwar ‘yan Shi’a da dama.
A zantawarsa da Buhari, Rouhani ya ce kar a yi amfani da wannan damar wajen haifar da rikicin addini kuma ya bukaci karin haske kan halin da shugaban Shi’a Sheik Ibrahim al-Zakzaky ke ciki.
Mahukuntan Iran sun bukaci gwamnatin Nijeriya da ta kula da lafiyar wadanda suka jikkata a tarzomar tare da biyan diyar barnar da sojojin kasar suka yi.
A ranar Talatar da ta gabata dubban mabiya mazhabar Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Tehran na Iran tare da nuna rashin jin dadin su kan kisan ‘yan Shi’a a Zaria.
Kazalika a Najeriya, mabiya Shi’an suna ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna, inda suka bukaci sojoji da su saki shugabansu Sheik Ibrahim al-Zakzaky yayin da rahotanni ke cewa jami’an ‘yan sanda sun bude musu wuta tare da kashe mutane hudu daga cikinsu.
Title :
Abin Da Shugaban Iran Ya Fadawa Buhari Akan Rikicin Yan Shi'a
Description : Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari ta waya, inda ya bukaci masaniya kan arangamar da ta auku tsakani...
Rating :
5