Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam dinda ke jikinta a kusa da wani masallaci a unguwar Ushari Bulabulin a Maiduguri ranar Litinin da safe.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa BBC cewa 'yar kunar bakin waken ta tayar da bam din ne a lokacin da ta kutsa kai inda ake binciken mutane wanda ke kusa da masallacin.
Mutane kimanin shida zuwa bakwai ne kuma suka jikkata a lokacin da bam din ya fashe in ji mazaunin unguwar.
Sai dai hukumomin soji ba su ce komai game da wannan sabon harin na baya-bayan nan ba.
Wannan hari dai na zuwa ne kasa da sa'oi 24 bayan da sojojin suka ce sun dakile wani hari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriyar shiyyar arewa maso gabas ta ce mutane 21 ne suka mutu, wadansu 91 kuma suka jikkata a harin na ranar Lahadi da yamma.
Title :
A Kalla Sama Da Mutane 20 Suka Rasa Rayukansu A Harin Yan Boko Haram A Maiduguri
Description : Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam dinda ke jikinta a kusa da wani masallaci a unguwar Ushar...
Rating :
5