Tambayoyi Da Amsa
Salam alaikum dafatan Mallam ya wuni lafiya, Mallam ina son a answer mun tambayata, mahaifiyarmu ce suka samu sabani da mahaifinmu har ta kai ga yace xai saketa, to shine wani malami yace mun wai asiri kishiyoyinta da mahaifiyar babanmu suka mata,saboda haka wai za'a bukaci kifi na hausa da mai kankara da kaza,da akuya ne ko ragu cikin biyun dai,sai a ambaci sunayensu wai a dafa daniyan duk Wanda ya mata Abu ya koma kansa.Tambayata shine hakan ya halatta ko kuma ya saba ma addini,idan bai hatta ba Mallam inason abani shawarar hanyar da zanbi domin gudun sabawa Allah.Nagode
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Hakika wannan Maganar tana kunshe da kusakurai da yawa. Babban Kuskure na farko shine wannan zargin da kukeyi. Domin shi zargi yana daga cikin mafiya miyagun laifuka.
Allah yana cewa : "HAKIKA SHI ZARGI BA YA WADATAR DA KOMAI DA KOMAI DAGA GASKIYA".
Kuma yace : "HAKIKA WANI SASHEN DAGA CIKIN ZATO, LAIFI NE".
Manzon Allah (saww) yace "HALAYE GUDA BIYU BABU ABINDA YA FISU MUNI : (SUNE) MUMMUNAN ZATO GA ALLAH, DA KUMA MUMMUNAN ZATO GA BAYIN ALLAH".
Don Haka bai halatta ku rika Zargin kishiyoyin mahaifiyarku akan abinda baku gani da idanunku ba. Koda kuwa akwai yiwuwar hakan. Wannan laifi ne babba wanda zai iya kaiku zuwa ga Hallaka.
Kuskure na biyu shine zuwa wajen 'Dan-Duba da kukayi. Domin bisa abinda wannan mutumin ya gaya muku, Kamar ya duba ne ya gano cewa asiri akayi.
Shi kuwa 'Dan duba bai halatta aje wajensa har ayi wata hulda dashi ba. Manzon Allah (saww) yace :
"DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KO DAN DUBA KUMA YA GASKATASHI AKAN ABINDA YA FADA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABINDA ANNABI MUHAMMADU (SAWW) YAZO DASHI".
Kinga anan kun aikata babban kuskure wanda zai iya kaiku ga kafirci. Wajibi ne ku tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki tun kafin azabarsa ta riskeku.
Kuskure na uku kuwa shine wadannan abubuwan da mutumin ya umurceku dasu duk basu halatta ku kawi masa ba. Domin kuwa watakil shi zai yi amfabi dasu ne domin Qulla nasa sihirin domin chutar da kishiyoyin mahaifiyarku.
Koda da gaske ne sunyi mata sihiri, to ai bai halatta kuje kuyi wani sihirin domin ramukon gayya ba. Wannan duk bai halatta ba. Domin sihiri kafirci ne.
Zargin da kuke yiwa Matayen Babanku da kuma Kakarku, zai iya janyo muku rashin Shiri atsakaninku. Kuma zai fusata Mahaifinku. Wannan zai janyo muku rashin albarka arayuwarku.
Ina baku shawarar cewa ku kyale wadancan abubuwan ku rungumi addu'a da nafilfili cikin dare. Sannan ku yawaita fadin :
"LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAAHIL 'ALIYYIL 'AZEEM". (100) A gurbin kowacce sallah, ko kuma safe da yamma.
Manzon Allah (saww) yace LA HAULA tana toshe kofofin bala'i ko bakin ciki guda saba'in. Kuma ita kanta taskar Aljannah ce.
Ku rika yawan maimaita Falaqi da naasi. Ku rika tawassuli dasu bisa niyyar karya sihirin (in ma akwaishi).
Ku rika yiwa mahaifiyarku nasiha akan hanyoyin da zata bi domin faranta zuciyar Mahaifinku da kyautata masa ako yaushe.
Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.
Title :
Zargin Kinshiyoyin Ta Sun Mata Asiri
Description : Tambayoyi Da Amsa Salam alaikum dafatan Mallam ya wuni lafiya, Mallam ina son a answer mun tambayata, mahaifiyarmu ce suka samu sabani da ...
Rating :
5