Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Solomon Arase, ya gargadi mutanen da ke shirin yin zanga-zanga domin neman ballewa daga kasar don kafa kasar Biafra da su kuka da kansu.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar, wacce wani kakakinta Olabisi Kolawole ya sanyawa hannu ta ambato Babban Sifeton ce, "Mun samu labarin da ke cewa wasu za su yi zanga-zanga da muggan makamai a sassa daban-daban na yankin kudu maso gabas. Hakan wani yunkuri ne na tayar da zaune tsaye don haka muna so a sani cewa dokar hana mallakar makamai ba bisa ka'ida ba na nan tana ci gaba da aiki".
Rundunar ta ce duk wanda ya nemi kawo hatsaniya kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba zai fuskanci fushinta.
Ta bukaci mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau-da-kullum, tana mai cewa za ta kare su daga duk wata barazana da ka iya tasowa.
Title :
Za mu murkushe 'yan Biafra — 'yan sanda
Description : Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Solomon Arase, ya gargadi mutanen da ke shirin yin zanga-zanga domin neman ballewa daga kasar don k...
Rating :
5