Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya nemi hukumar tsaro ta farin kaya, DSS da takwararta da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin kasa ta'annati, EFCC su kama masu gidajen man da ke boye fetur.
Kamfanin NNPC ya ce ya nemi agajin hukumomin biyu ne a yunkurin da yake yi na magance matsalar man fetur da ake fama da ita a sassa daban-daban na kasar.
A wata sanarwa da kakakin kamfanin, Ohi Alegbe ya fitar, NNPC ya nemi afuwar 'yan Najeriya saboda wahalar da suke sha kafin samun man fetur, yana mai cewa yana daukar kwararan matakai domin shawo kan matsalar.
Sanarwar ta kara da cewa, "Mun nemi agajin EFCC da DSS domin su sanya idanu sosai kan gidajen man da ke boye shi, kuma za su kama duk wanda aka samu yana boye man."
Title :
Za A Fara Kama Masu Boye Fetur A Najeriya
Description : Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya nemi hukumar tsaro ta farin kaya, DSS da takwararta da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin ...
Rating :
5