• Shinkafa
• Alaiyahu ko Zogale
• Albasa Attaruhu
• Kifi
• Nama
• Mai
• White pepper
• Curry
• Maggi&Gishiri
Dama kin gyara shinkafar ki an barzo miki a inji sai ki dafa namanki da citta da albasa ki farfasashi kamar zakiyi dambu,ki jajjaga attaruhu da albasa ki yanka alayyahu ko ki gyara zogale,sai ki daka gyada sai ki zubawa shinkafar ruwa wato ki yayyafa ko ina,sai ki tirarata a gittere,idan ya tirara kamar 30min saiki sauke ki juye a kwano ki zuba kayan hadinnan da kifi idan kina so da maggi da curry white pepper gishiri da mai ki jujjuya sai ki mayar ki kuma turarawa,idan yayi zakiga yayi laushi kuma kamshi zai ta tashi,saiki sauke.
(JuMa'Ah MuBaRaKaH)
Admn Asma'u