¤¤¤CHICKEN BALLS IN BATTER¤¤¤
• Tsokar Kaza
• Fulawa
• Baking powder
• Kwai
• Magi&gishiri
• Mai
• Mmadara
• Koran tattasai
• Albasa, citta
YADDA AKEYI
Zaki dafa kaza da magi da gishiri da garin citta da albasa ta dahu sosai,sai ki zare kashin a daka tsokar a turmi,ki aje agefe,sai ki yanka albasa da koran tattasai kanana,sai ki kwaba fulawa da baking powder ko kuma ita kadai duk yadda kikayi zeyi,amma kamar kwabin waina,sai ki dauko hadin nan na kaza da kwai madara koran tattasai magi da gishiri ki cakudasu har komai ya hadu idanma kina son attaruhu kina iya sawa,saiki cuccurata kamar yadda kika gani a hoto,
saiki dinga tsomawa fulawa kina soyawa,sai aci.