• Kifi
• magi gishiri
• mai
• kayan kamshi
• tafarnuwa
• albasa
zaki wanke kifinki sosai ki ajeshi ya tsane,sai ki jajjaga kayan miyarki idan kuma markadene shikenan to saiki zuba a tukunya ki dan sa mai kadan idan ya tafaso saiki tsaida ruwa,ki zuba kayan kamshi magi da gishiri da albasa ko tafarnuwa ki barshi ya dahu,idan ruwan ya ragu ma'ana ya fara qonewa sai ki kawo kifin ki saka a hankali,ki rage wuta don karya farfashe,kuma karki yawaita juyawa,haka zaki barshi har ya dahu,zakiji kamshinsa yana tashi,sai ki sauke.zaki iyaci da komai.