Rahotanni daga garin Banburatai da ke karamar hukumar Biu a jihar Borno na cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar BH ne sun kai hari garin.
Lamarin dai ya faru ne tun a daren ranar Asabar, amma saboda rashin kyawun hanyar sadarwa rahotanni ba su fito ba sai a ranar Litinin.
Ganau sun shaida wa BBC cewa maharan sun kona wani bangare na garin tare da kona wasu motoci na farar hula guda shida, da kuma yin awon gaba da mata da kananan yara a cikin motoci uku da suka sace.
Haka kuma mutanen garin sun ce maharan sun zo ne a kan kekuna da babura, wasu kuma a kafa.
Sai dai sun yi korafin cewa babu jami'in tsaro ko guda a lokacin da aka kai harin.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin, inda ta ce tuni dakarunta suka fantsama daji domin bin sahun maharan.
Title :
Yan Boko Haram Sun Sace Wasu Mata A Banburaitai
Description : Rahotanni daga garin Banburatai da ke karamar hukumar Biu a jihar Borno na cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar BH ne sun kai h...
Rating :
5