Al’ummar Shekarbarde Baranda wadda ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun shaida wani al’amari mai ban tsoro, inda wani magidanci mai suna Alhaji Ado Mai Siminti ya dauki wuka kuma ya daba a wuyansa, hakan tasa ya yanke makogoronsa baki daya.
Wannan bawan Allah dai da safiyar ranar Talatar da ta gabata ne ya dauki wuka, kuma ya fada cikin bandaki inda ya datse makoshin nasa, ganin yadda ya shigo da gudu tare da wuka a hannunsa yasa jama’a tare da iyalinsa suka bishi bandakin, amma ya riga ya rufe sai karya kofar aka yi kafin a isa har ya aikata wannan ta’annaci.
Kokarin karbe wukar daga hannunsa ne ya yi sanadiyyar yankar wani mutun guda a hannu. An garzaya da shi asibiti, amma tun kafin a isa asibitin rai yayi halinsa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Kano Magaji Musa Majiya ya tabbatarwa da wakilinmu faruwar wannan al’amari, ya kuma bayyana cewar suna nan suna ci gaba da bincike domin tabbatar da dalilin aikata wannan aika-aika.
Shi dai Alhaji Musa kamar yadda bincike ya nuna sana’ar gina gidaje yake yana sayarwa, daga baya ya gamu da karayar arziki wanda har takai ana zargin hankalinsa ya tabu, amma dai jama’a sun shaida Alhaji Ado a matsayin mutumin kirki, mai taimakon jama’a ga kuma juriyar wajen tallafawa leburori dake aiki a karkashinsa, saboda haka wasu ke tunanin kila matsin lambar yawaitar ba shi ne ya yi sandiyyar gushewar hankalinsa wanda hakan ya yi sanadiyar aikata wannan aika-aika.
Tuni akayi jana’izarsa kamar yadda addinin Islama ya tsara.
Title :
Yadda Wani Attajiri Ya Yi Wa Kansa Yankan Rago A Jihar Kano
Description : Al’ummar Shekarbarde Baranda wadda ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun shaida wani al’amari mai ban tsoro, inda wani magidanci mai ...
Rating :
5