Wata kungiya mai suna, Zauren Dattawan Arewa (NEC), ta gargadi Shugaba Muhammadu Buhari akan ramuwar siyasa da sunan yaki da rashawa.
Kungiyar tayi Allah wadai da abunda Buhari yake yi inda ya bayyana ra’ayin ta a Kano, a ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba. Shugaban kungiyar Tanko Yakasai ne ya bayyana haka. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Yace: “Abunda sabuwar gwamnati take yi ta hanyar yan siyasa da jami’an tsaro ba wani abun azo a gani bane. ” Tanko Yakasai yayi Allah wadai da yadda gwamnatin Buhari tayi ma Sambo Dasuki. Ya bayyana cewa, mutanen Najeriya sun fara jin cewa Buhari dan kama karya ne.
A watan daya wuce, Yakasai ya shiga wata tattaunawa a Channels TV inda ya bayyana cewa: “Ni bani goyon bayan Buhari.” Ya kuma bayyana cewa Buhari ya dawo kan mulki ne don yaci mutuncin majiyar shi.