Jami'an kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an sake samun wani mutum dauke da cutar Ebola a Liberia, kasa da watanni uku bayan da aka ce babu cutar a kasar.
Yaron da aka samu na dauke da cutar mai shekaru 10 ne kuma yana zaune ne a wata unguwar marasa galihu a Monrovia, babban birnin kasar.
Wannan labarin wani koma baya ne ga kasar inda aka samu sama da mutane dubu 10 da suka kamu da cutar kuma sama da dubu 4 suka mutu tun lokacin da aka gano cutar a kasar.
A watan Mayu ne aka fara cewa cutar ta bar kasar amma bayan wata daya sai ta sake dawowa.
A farkon watannan ne aka ce cutar ta bar Saliyo.